Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: CBS News ta bayyana cewa Trump ya fara tattaunawa da mashawartansa kan yiwuwar maye gurbin ministan tsaro Pete Hegseth, bayan manyan asarar da jam'iyyar Republican ta sha a zaɓen tsakiyar wa'adi na Majalisa.
Bisa ga rahoton, sakamakon yaƙin kan Iran na iya kai wa kwamandan rundunar tsakiya ta Amurka, Brad Cooper, da shugaban hafsan haɗin gwiwa, Dan Caine, saboda rawar da suka taka wajin bayar da shawarwarin soji a lokacin yaƙin.
Majiyoyin Republican sun gabatar da sunan gwamnan jihar Florida Ron DeSantis a matsayin yiwuwar maye gurbin Hegseth. DeSantis ɗan siyasar Republican ne mai shekaru 48, wanda a baya ya kasance hafsan shari'a a sojin ruwan Amurka, kuma an tura shi lardin Al-Anbar a shekarar 2007, inda ya ba da tallafin shari'a ga ayyukan sojojin musamman na Amurka.
Duk da waɗannan tsokaci, Fadar White House ta tabbatar da cewa Trump har yanzu yana da cikakken amincewa ga Hegseth, kuma ba a yanke wata shawara a hukumance kan maye gurbinsa ba.
………………
Ra'ayinka